Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bashin da ake bin Najeriya ya karu zuwa sama da Naira tiriliyan 46- DMO

Published

on

  • DMO ta koka dangane da karuwar bashin da ake bi kasar nan.
  • Bashin da ya kai yawan Naira tiriliyon 46.
  • Hakan ya samo asali ne biyo bayan yadda gwamnatin tarayya da ta jihohi ke sake ciyo sabbin basuka.
  • Ofishin Kula da basuka a Najeriya DMO ya ce, bashin da ake bin Najeriya ya karu zuwa sama da Naira tiriliyan 46 a watan Disambar 2022 da ya gabata.

A wata sanarwa da Ofishin ya fitar a jiya Alhamis, ‘ya ce an samu ƙarin tiriliyan bakwai cikin basukan da ake bin ƙasar nan biyo bayan yadda gwamnatin tarayya da ta jihohi ke sake ciyo sabbin basuka domin gudanar da manyan ayyuka da kuma cike gibin kasafin kuɗi’.

Ofishin ya kuma ce, ‘kokarin da gwamnati ke yi na ƙara samun kuɗaɗen shiga daga ɓangaren albarkatun man fetur, da kuma ɓangarorin da ba na man ba, za su taimaka wajen gudanar da ayyuka ba tare da cin bashi ba’.

‘A shekarar 2005 ne ƙasar nan ta cimma wata yarjejeniyar yafiyar bashi da ƙungiyar Paris Club, abin da ya sanya aka yafe mata dala biliyan 18 daga cikin bashin da ake binta’.

Rahoton: Madeena Shehu Hausawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!