Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bata gari sun addabi yankin mu – Kwamitin cigaban Farawa

Published

on

Kwamitin cigaban al’ummar garin Farawa da ke karamar hukumar Kumbotso a nan Kano ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu bata-garin matasa suka addabi yankin na su tare da jefa al’umma cikin halin fargaba.

Shugaban kwamitin Alhaji Adamu Dahiru Farawa ne ya bayyana hakan lokacin da yake jan hankalin al’ummar yankin domin ganin sun mayar da hankali wajen samawa kansu tsaro musamman ma a tsakanin matasa.

Ya kara da cewa kwamitin ya samu rahotannin yadda wasu bata-gari ke haurawa gidajen mutane cikin dare tare da yi musu sace-sace da kuma yi musu barazana da lafiyarsu, yana mai cewar wajibi ne su tallafawa jami’an tsaro ta hanyar sanya ido sosai da kuma bayar da rahotann.

Alhaji Adamu Dahiru Farawa ya kuma bukaci rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ta kara musu jami’an tsaro a yankin don magance matsalar da suke fuskanta.

Wakilinmu Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa al’ummar garin na cikin halin damuwa da fargaba da zarar magriba ta yi, inda suka yi kira ga mawadatan da ke cikinsu da su taimakawa ‘yan kwamitin da kayan aiki.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!