Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda aka yi mumunan hadarin mota a Kano

Published

on

A dazu ne wani mumunan hadarin mota ya afko a yankin kofar Kabuga dake karamar hukumar Gwale a nan Kano.

Hadarin dai ya afko ne akan hanyar zuwa Jami’ar Yusuf Mataima Sule bayan da wasu motoci uku suka yi taho mu gama.

A inda wata karamar mota kirar toyo Corolla tare da wani kan DAF ,suka yi taho mu gama Toyota Corrolla din ta kifa sakamakon dukan da kan DAF din tayi mata ta gefen ta, kamar yadda wani da abun ya faru a gaban idon su ya shaidawa Wakilin mu Hassan Auwalu Muhammad

Shima mai karamar motar ta corrolla, wanda dakyar aka zaro shi daga cikin motar, sakamakon kifawar da tayi, yayi mana karin haske akan yadda abun ya faru yana mai cewa shima tsintar kan sa ya yi kamar mafarki

Wakilin na mu ya yi kokarin jin ta bakin direbobin DAF din, amman sun ki yarda ya dauki muryar su, to amman wani da yake cikin daya daga cikin motocin DAF din ya ce Allah ne ya kaddara haka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!