Labarai
Bauchi: Yan Sanda sun kama mutane 3 da ake zargi da hannu a kisan kai

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a wani kisan kai da ya faru a karamar hukumar Zaki.
Hakan na kunshe a cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Nafiu Habib ya fitar a yau Talata.
Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 15 ga Maris 2026, inda aka kashe wani mutum mai suna Saleh Ibrahim mai shekaru 35 da makami mai kaifi yayin da yake tafiya a kan babur, sannan aka sace babur dinsa.
Sanarwar ta kara da cewa bayan faruwar lamarin, wasu mazauna yankin sun yi zanga-zanga tare da kona gidaje a kauyen Jamaʼaren Fulani, lamarin da ya janyo jikkata wasu mutane ciki har da jami’an tsaro.
Haka zalika Sanarwar ta ce binciken da aka gudanar ya kai ga cafke Muhammad Jauro Haladu Yako mai shekaru 28, Muhammad Wito mai shekaru 27, da Ibrahim Muhammad mai shekaru 19, dukkansu daga kauyen Alagarno da ke karamar hukumar ta Zaki.
You must be logged in to post a comment Login