Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bauchi:gwamna mai barin gado ya amince da shan kaye

Published

on

Gwamnan jihar Bauchi mai barin gado Muhammad Abdullahi Abubakar ya amince da shan kaye tare da ta ya sabon zababben gwamnan jihar ta Bauchi Sanata Bala Muhammed nasarar da ya samu.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnan Ali Muhammed Ali.

 

Sanarwar ta ce duk da irin zazzafar yakin neman zabe da ya gudana tsakanin manyan jam’iyyun jihar guda biyu, amma an gudanar da zaben cikin lumana ba tare da zub da jini ba.

 

Gwamna Muhammed Abdullahi Abubakar ta cikin sanarwar ya kuma gayyaci sabon gwamnan Sanata Bala Muhammed da ya zo su zauna domin tsara yadda za a gudanar da tsare-tsaren mika mulki a watan Mayu.

 

Sanarwar ta kuma ruwaito gwamnan na godewa al’ummar jihar Bauchi sakamakon hadin kai da suka bai wa gwamnatin sa tare da yin kira garesu da su ba da hadin kai ga sabon gwamnan da zai gajeshi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!