Connect with us

Labarai

An sako makaranci Alkur’anin nan Sheikh Ahmad Suleiman

Published

on

An sako fitaccen makarancin Alkur’anin nan Sheikh Ahmad Suleiman, wanda wasu ‘yan bindiga su ka sace shi da abokan tafiyar sa a kwanakin baya.

 

A yayin zantawa da gidan rediyo freedom ta wayar tarho wani makusancin Shehin Malamin, Alaramma Isma’il Maiduguri ya ce an sako Sheikh Ahmad Suleiman kuma yana cikin koshin lafiya.

 

A cewar sa, Shehin Malamin tare da abokan tafiyar sa suna kan hanyar su ta zuwa Kano daga inda ‘yan bindigar suka boye su.

 

 

Rahotanni sun ce, wasu ‘yan bindiga ne suka sace Sheikh Ahmad Suleiman tare da wasu mutane biyar, kwanaki goma sha uku da suka gabata akan titin da ya hada garuruwan Sheme da Kankara a jihar Katsina.

 

Shi dai Sheikh Ahmad Suleiman da sauran mutanen biyar suna kan hanyar su ta zuwa Kano daga birnin Kebbi babban birnin jihar Kebbi lokacin da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,834 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!