Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bayan dakatar da Muhyi Ganduje ya naɗa sabon shugaban hukumar Anti kwarafshin

Published

on

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Barrista Mahmud Balarabe a matsayin mai riƙon mukamin shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.

 

Hakan na cikin wata sanarwa ce mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labarai na gwamnan Kano Abba Anwar.

 

A cewar sanarwar naɗin Barrista Mahmud Balarabe ya fara aiki ne nan take.

 

Kafin naɗin nasa darakta ne mai kula da harkokin shigar da kara a ma’aikatar shari’a ta jihar Kano.

 

A baya-bayan nan ne majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugaban hukumar ta Anti Corruption ta jihar Kano, Barrista Muhyi Magaji Rimingado.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!