Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NCC ta wayar da kan al’umma dangane da sabunta rijistar layikan waya a Kano

Published

on

Hukumar sadarwa ta kasa NCC ta gabatar da wani taro anan Kano dan kawo karshen korafe-korafen da mutane sukeyi dangane da sabunta rijistar layikan waya.

Shugaban shiyya na hukumar, Alhaji Shu’aibu Sadi da ya jagoranci taron, ya ce, an gudanar da taron ne dan inganta harkar sadarwa a fadin kasar nan.

Shima shugaban kungiyar masu yin rijista da saya da layikan waya, kwamared Sulaiman Ya’u Sulaiman, ya bayyana cewar daga lokacin da aka dakatar da yin rijistar layikan waya a kasar nan mutanen su suka shiga mawiyacin hali.

Ya Kuma ce, yanzu haka kungiyar tasu ta cika dukkanin ka’idojin da hukumar sadarwa ta kasa ta sanya wajen yin rijista da sayar da layikan waya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!