Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Bayan sauyin filin wasa: Kano Pillars tayi nasara akan Nassarawa United

Published

on

Zakarun gasar Firimiya ta kasa  har sau hudu a baya, Kano Pillars tayi nasarar doke Nassarawa United da ci biyu da nema a wasan gasar NFPL.

Kano Pillars ta fafata wasan a filin Muhammad Dikko da ke jihar Katsina, wanda shi ne sabon filin wasa da zata rika buga wasanta na gida.

Wasan dai shi ne mako na 18 da aka gudanar a ranar Lahadi 06 ga Maris din 2022.

Tin da fari dan wasa Mark Daniel ne ya fara zura kwallon farko a minti na 1 da wasan, bayan samun taimako daga hannun Rabiu Ali Pele.

A minti na 41 shima dan wasa Efeanyi ya kara kwallo ta biyu ga kungiyarsa ta Kano Pillars dab da za aje hutun rabin lokaci.

Kafin wannan wasan dai Kano Pillars na mataki na 14 da maki 18, wanda kawo yanzu jumulla tana da maki 21 a wasanni 18 da ta fafata a kakar wasannin shekarar 2021/2022.

Filin wasa na Muhammad Dikko dai, shi ne sabon filin wasan da Pillars ta koma buga wasa, bayan tin da fari tana bugawa a garin Kaduna a filin Ahmadu Bello.

Hakan da ya sanya da dama daga cikin magoya bayanta ke sukar lamarin komawa jihar ta Katsina da buga wasanta na gida.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!