Labaran Wasanni
Bayern ta lashe gasar Bundesliga karo na 8 a Jere

Kungiyar Kwallon kafa ta Bayern Munich, ta zama zakaran gasar Bundesliga na kasar Jamus (Germany ) na bana, kuma karo na takwas a jere.
Bayern Munich , ta samu nasarar ne jim kadan bayan ta doke takwarar ta , ta Werder Bremen da ci daya mai ban haushi.
Wasan wanda aka fafata a gidan kungiyar ta Werder Bremen , wanda dan wasa Robert Lewondowski ya jefa Kwallo daya tilo data baiwa kungiyar tashi nasara a minti na 43 kafin tafiya hutun rabin Lokaci.
Kwallon ta Lewondowski , ita ce Kwallon sa ta 31 a gasar ta Bundesliga na bana,nasarar ta Bayern Munich ta kasance ta takwas a jere , tun daga shekarar 2012 kawo ya zuwa yanzu.
You must be logged in to post a comment Login