Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Benue:A yanzu akalla mutane 45 ne suka rasa rayukansu a gobarar motar man fetur

Published

on

Adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon gobarar da ta tashi a wata motar dakon man fetur da ta yi hatsari a jihar Benue ya karu zuwa arba’in da biyar.

 

Haka zalika wasu mutane dari da daya sun samu munanan raunuka ciki har da wata mata mai dauke da juna biyu da kananan yara biyu sanadiyar gobarar da ta tashi a yankin karamar Hukumar Gwer ta gabas a jihar ta Benue.

 

Kwamandan Hukumar kiyaye abkuwar hadura ta kasa reshen jihar Benue, Aliyu Baba, ya tabbatar da adadin wadanda suka rasa rayukansun , yana mai cewa tuni jami’an Hukumar suka kwashe su zuwa Asibiti.

 

Aliyu Baba ya kuma ce shi da sauran jami’an Hukumar ta (FRSC) sun kwashe tsawon awanni wasunsu ma sun kwana a wajen da lamarin ya faru domin ci gaba da ayyukan jin kai.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!