Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaba Buhari ya jaddada matsayinsa na nada mutane na gari a gwamnatinsa

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara jaddada matsayin sa na tabbatar da nada mutane na gari a kunshin gwamnatin sa zango na biyu.

 

Muhammadu Buhari ya ce yana fata wadanda zai nada a zango na biyun zasu ba da gudunmawa wajen cika alkawuran da ya daukarwa al’ummar kasar nan yayin yakin neman zabe.

 

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a jiya Talata lokacin da ya ke ganawa da ‘yan kungiyar Buhari Media Organization wadanda suka kai masa ziyara fadar Asorok.

 

Ya ce ya sha matukar wahala wajen tallata ayyukan da gwamnatin sa ke yi cikin shekaru hudu da suka gabata sakamakon wasu manufofi da ayyukan da ya gabatar wadanda ba su yi dadi ba ga wasu al’ummar kasar nan.

 

Shugaban kasar ya ce wasu na ganin kamata yayi a ce wata guda bayan rantsuwar wa’adin mulki, shugaba ya sanar da ministocin da zayyi aiki da su, sai dai ya ce, damuwar sa shine samar da kunshin ministoci da za su taimakawa wajen kyautatu lamura a kasar nan

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!