Connect with us

Labarai

Benue:Mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon gobarar tankar man fetur

Published

on

Mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon wata gobarar tankar man fetur da ta tashi a kauyen Ahmube da ke yankin karamar Hukumar Gwer ta gabas da ke jihar Benue.

 

Wani shidar gani da ido mai suna Mr. Austin Nembe, ya shaidawa manema labarai cewa, tankar makare da man fetur wadda ta fito daga yankin kudu maso gabashin kasar nan, tana kan hanyar zuwa garin Makurdi babban birnin jihar Benue ta fadi sannan ta kama da wuta biyo bayan neman kaucewa ramin kan titi da direbar tankar ya yi.

 

A cewar sa bayan faduwar tankar man ke da wuya, sai mazauna kauyen su ka fara kwashe man fetur din tankar da ke ta kwarara wanda kuma ba tare da bata lokaci ba, ta kama da wuta, inda mutane da dama suka kone kurmus.

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ta ce, bata kai ga tattara alkaluman wadanda gobarar ta shafa ba.

 

Mai Magana da yawun rundunar Catherine Anene, ta ce, babban jami’in dan sanda da ke Aliade, ya sanar da shalkwatar ‘yan sandan da ke Makurdi cewa, bayan faduwar motar, sun gargadi mutanen kauyen game da hatsarin da ke tattare da kwasar man da su ke yi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!