Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gobarar tankar mai ta hallaka mutane 12 – FRSC

Published

on

Akalla mutane 12 ne suka rasa rayukansu sakamakon wata gobara da ta tashi a motar dakon mai a kauyen Oshigbude da ke yankin karamar hukumar Agatu a jihar Benue.

 

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a jiya lahadi, bayan da motar ta fadi a mahadar titin kauyen wanda dalilin haka mai ya kwaranye.

 

Da ya ke jawabi kan faruwar gobarar, shugaban hukumar dakile abkuwar hadurra ta kasa reshen jihar Benue, Yakubu Muhammed, ya ce, direbar motar ya kasa shawo kan motar ce, lokacin da ya zo juyawa, wanda sanadiyar hakan motar ta fadi.

 

A cewar sa, cikin wadanda suka mutun sun hada da: maza takwas da mata uku da kuma wani kankanin yaro.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!