Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Barka Da Hantsi

Bikin ranar haɗa magani: Za mu tabbatar da ingancin magani kafin fitar da shi kasuwa – Malam Ahmad

Published

on

Ƙungiyar masu fasahar haɗa magunguna ta ƙasa ta ce, duk wani magani da aka haɗa shi, sai an fara gwada shi a kan dabbobi kafin mutane.

Shugaban ƙungiyar reshan jihar kano Malam Ahmad Yusuf ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Hnatsi na Freedom Radio.

Shirin wanda ya mayar da hankali kan bikin ranar haɗa magunguna wanda majalisar ɗinkin duniya ta ware talata ta uku a watan Oktoba don yin bikin.

Malam Ahmad Yusuf ya ce “ Ƙungiyar mu na ba da gudunmawa wajen hada magani ga marasa ƙarfi da kuma samar da shi a farashi mai sauƙi baya ga samar da shi mai inganci yadda ake buƙata”.

“kamata yayi matune su riƙa amfani da magunguna masu kyau sannan su riƙa bincikawa ayayin don sanin lokacin da ya ɗauka a kasuwar, amma dai muna fuskantar kalubale na rashin yin binkice mai zurfu da kuma rashin zurfafa ilima ga masu sayar da magani” in ji Ahmad.

Malam Ahmad Yusuf ya buƙaci al’umma da su mayar da hankali wajen sayen magunguna masu kyau a guraren da ya dace.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!