Connect with us

Labarai

Bikin samun ƴancin kai: Gwamnatin tarayya za ta rufe wasu sashi na sakatariyar Abuja

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce za ta rufe wani sashi na sakatariyar gwamnatin tarayya da ke Abuja tun daren ranar Alhamis mai zuwa.

Wannan dai na zuwa ne a wani bangare na ingata tsaro gabannin bikin ranar samun ƴancin kai da zai gudana ranar Juma’a karo na 61.

Shugabar ma’aikatar gwamnatin tarayya Folashade Yemi Easan ce ta bayyana hakan ga maneman labarai a birnin tarayya Abuja.

A cewarta dukkanin dogayen gine-ginen da ke kallon filin taro na Eagle square na daga cikin ofisoshin da za a rufe kai tsaye.

Sai dai ta ce rufewar ba ta shafi wasu daga cikin gine-ginen ma’aikatar ba, musamman wadanda basa kallon filin taron.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!