Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Inganta muhalli: Za mu samar da hukumar kula sauyin yanayi – Dakta Getso

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce, za ta samar da hukumar kula sauyin yanayi a jihar.

Kwamishinan muhalli, Dr. Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga kungiyoyin da ke fafutukar kare muhalli a karkashin haɗakar kungiyoyi masu zaman kan su, da ke wayar da kai ga me da sauyin yanayi.

Dakta Getso ya ce matular aka samar da hukumar za ta mayar da hankali kan magance abubuwan da suke haifar da sauyin yanayi, da kuma kawo ƙarshen ayyukan sare bishiyoyi, da zaizayar ƙasa da sauran matsalolin da ƙasa ke fuskanta.

Tsaftar muhalli: An rufe kamfanin ɗura iskar gas a Challawa

Kwamishinan ya ce “ma’aikatar muhalli tana kan aiwatar da dokar kula da sauyin yanayi da ta gandun daji wadda ke gaban Kwamishinan shari’a kuma da zarar ya sanya hannu za a miƙa ta gaban majalisar dokoki domin sahalewa”.

Getso ya yabawa haɗakar ƙungiyoyin bisa jajircewar su wajen ganin an inganta muhalli.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!