Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

Tsaro: Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane 8 a Kaduna

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce wasu da ake zargin ‘yan fashi ne sun kashe mutane takwas tare da jikkata wasu hudu a wasu hare-hare daban-daban a kananan hukumomin Chikun, Giwa da Kajuru da ke jihar.

Kwamishinan tsaron da harkokin cikin gida Samuel Aruwan ne ya tabbatar da harin ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Harin na zuwa ne yayin da ‘yan fashin suka harbi wata mota lamarin da ya haifar da kifewarta nan take.

Sanarwar ta kuma ce, ‘yan fashin sun kai wani hari kan mutane a Iburu da ke cikin Karamar Hukumar Kajuru kuma sun kashe mutum daya, yayin da kuma suka mamaye kauyen Hayin Kanwa da ke gundumar Fatika, a karamar hukumar Giwa suka kashe wani dan kasuwa bayan ya bijirewa yunkurin sace shi da suka yi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!