Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Borussia Dortmund: Ba za mu sayar da Sancho ba

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund ta tabbatar da dan wasa Jadon Sancho zai ci gaba da zama a kungiyar.

Hakan ya biyo bayan yunkuri da Manchester United ta yi kan daukar dan wasan.

 Manchester United dai ta baza komar ta tare da nuna maitar ta a fili, yayin da take ganin dan wasan yafi dacewa da kungiyar fiye da kowace kungiya, amma sai dai hakar ta ba ta cimma ruwa ba.

Jadon Sancho, dan kasar Ingila mai shekaru 26, da Dortmund ta sayo daga Manchester City kan Yuro miliyan 10 a shekarar 2017, yanzu haka ta na neman a bata Yuro miliyan 100 a kan dan wasan.

Kawo yanzu dai United ta fara hakura da zawarcin na Sancho, inda kungiyar ta kuma ci gaba da shinshina dan wasan Real Madrid Gareth Bale da na Inter Milan Ivan Perisic.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!