Connect with us

Labaran Wasanni

Eric Dier: Mourinho ne kwarin zama na a Tottenham

Published

on

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur, Eric Dier, ya ce mai horas da kungiyar Jose Mourinho ne ya bashi kwarin gwiwar ci gaba da zama a kungiyar.

Dier dan kasar Ingila, ya dai amince da sabon kwantiragin shekara hudu da Tottenham ta bas hi dama a watan Yulin da ta gabata na shekarar da muke ciki.

Amincewar sa da sabon kwangiragin, ya kawo karshen jita-jitar cewa zai fice daga kungiyar bayan da kwantiragin sa na shekaru shida ya kare.

Dan wasan mai shekara 26, ya na taka leda ne a tsakiyar Tottenham Hotspur kafin ya zama dan wasan baya a kungiyar, bayan da Mourinho ya maye gurbin Pochettino.

Eric Dier dai ya jinjinawa Jose Mourinho da ya bashi damar yin wasa a gurbin da yake tinanin shi ne yafi dacewa dashi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 331,771 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!