Labarai
Bruno Fernandes ya koma Manchester United
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United dake kasar Ingila ta tabbatar da daukar dan wasa Bruno Fernandez daga kungiyar kwallon kafa ta Sporting Lisbon dake Kasar Portugal.
Bruno Farnandez ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyar da rabi, akan Fam Miliyan hamsin da biyar, Inda yake da damar karawa idan har kwantiragin idan ya kare.
Bruno mai shekaru 25 a duniya, ya bugawa Kasar Portugal wasanni 137, inda ya zura kwallaye 63, sannan ya taimaka aka zura kwallaye 52.
Kuma yana cikin jerin yan wasan da suka lashe gasar UEFA Nations Cup League a 2019, wato kofin kasashen nahiyar turai.
Da yake jawabi, sabon dan wasan ya bayyana jin dadinsa a da kasancewa a kungiyar ta Manchester United, inda ya bayyana cewa, ya kasance masoyin Manchester United tun zamanin da Cristiano Ronaldo yake jan zarensa a kungiyar.
Ya kara da cewa zai yi iya kokarinsa wajen ganin Manchester ta samu nasarori da dama, musamman ma a kakar wasanni ta bana.