Labarai
Zamu baiwa sabbin ‘yan sanda na sa kai horo- Sarauniya
Rundunar ‘yan sandan Sarauniya ta jihar Kano, ta ce, za ta ba da cikakken horo ga sababbin ‘yan sandan na sa kai da aka fi sani da ‘yan sandan sarauniya wadanda za ta dauke su aiki.
Kwamandan rundunar ‘yan sandan na Sarauniya, Alhaji Muhammad Bello Dalha ne ya bayyana haka, bayan kammala shirin barka da hansti na nan tashar freedom rediyo da safiyar yau Juma’a.
Ya ce, za a basu horo ne don ganin sun samu kwarewa wajen tafiyar da aikinsu kamar yadda ya kamata.
Muhammad Bello Dalha, ya kuma ce, za a bi hanyoyin da ya kamata, wajen tantance sababanin ‘yan sandan na sa kai don ganin cewa, ba a dauki baragurbi ba.
Kwamandan ‘yan sandan Sarauniyar, ya kuma bukaci duk wanda ya tsinci kansa cikin sababbin ‘yan sandan, da su kasance masu gaskiya da rikon amana tare da cire son zuciya wajen gudanar da aikin su.
Alhaji Muhammad Bello, ya ce, tsarin daukar sababbin jami’an ‘yan sandan na Sarauniya, za a gudanar da shi ne nan gaba kadan bada jimawa ba.