Labarai
Budurwa ta kashe saurayinta kan Naira 1, 500
Budurwar mai shekaru 28 mai suna Ebiere Ezikiel ta cakawa saurayinta mai suna Godgift Aboh wuka bayan da ya mareta kan tuhumarsa da ta yi game da makomar kudinta 1,500 da ta ce an sace.
Lamarin dai ya faru ne a unguwar Obele da ke yankin karamar hukumar Yenagoa a jihar Bayelsa.
Wasu makusantan masoyan biyu sun ce sun kwashe tsawon shekara daya suna soyayya da juna kafin ibtila’in ya faru tsakaninsu.
Ezikiel wadda ta shaidawa manema labarai yadda abin ya faru bayan da rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa ta yi holenta a garin Yenagoa tare da wasu masu aikata laifuka daban-daban da suka hada da: masu garkuwa da mutane da barayi da kuma masu fasa butun mai, ta ce, ta yi nadamar hallaka saurayin nata kan abin da bai kai ya kawo ba.
‘‘Rashin fahimta ne ya faru tsakani na da shi, amma ni da shi masoya ne, muna son juna sosai, kudi na ne Naira 1,500 suka bata da na tambaye shi, sai kawai ya mare ni, lamarin da ya sa na fusata sai na caka mishi wuka,’’ inji Ebiere Ezekiel.
A bangare guda kuma Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Bayelsa Mike Okoli ya kuma yi holen wani saurayi mai suna Promise Okoli da ake zargi da kashe budurwarsa mai suna Esther Uko bayan da ya sharara mata mari sau biyu.
You must be logged in to post a comment Login