Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari na ganawa da shugabannin tsaron ƙasar nan

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na wata ganawa da shugabannin tsaron kasar nan a fadar sa da ke Villa a Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa shugaba Buhari zai saurari wasu bayanai kan sha’anin tsaro daga babban hafsan sojin kasar nan Janar Lucky Irabor da Sufeton yan sanda Usman Allƙali Baba da sauran shugabannin tsaro.

Cikin waɗanda suka halarci zaman sun haɗar da, ministan tsaro Manjo janar Bashir Salihi Magshi mai ritaya, da ministan shari’a Abubakar Malami, da mai kula da ayyukan yan sanda Maigari Dingyaɗi.

Sauran sun haɗa da ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola da kuma ministan harkokin ƙasashen waje Geaffrey Onyeama.

Ana sa ran ganawar ta su, za su yiwa shugaba Buhari bayani kan yanyin tsaron ƙasar a halin yanzu, kamar yadda mashawarcin sa Femi Adesina ya bayyana a shafin sa na Facebook.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!