Labarai
Buhari ya aike da bukatar majalisar dattijai ta sahale da karin kwarya kwaryar kasafin kudin bana
![](https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2019/09/Buhari-at-United-asem.jpg)
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi majalisar dattijai da ta sahalewa da kudirin da ya aike mata na karin kwarya-kwaryar kasafin kudin bana.
Shugaban majalisar dattaijai sanata Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar a zaman majalisar na yau.
Kudirin ya nuna cewa za’a ware wani kason kudin domin sayo makamai a wani bangare na yaki da ta’addanci da kuma tashe-tashen hankula a kasar nan.
Haka kuma gwamnatin tarayya ta ce tana bukatar karin kason kudin ne domin sayen alluarar rigakafin cutar Covid-19 da kuma wasu kayayyaki a bangaren kiwon lafiya.
You must be logged in to post a comment Login