Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya amince da bai wa gidajen Rediyo da Talabijin 159 lasisi

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da bai wa gidajen Redio da Talabijin guda 159 lasisi, don fara aiki a ƙasar nan.

Shugaban hukumar kula da kafafen yaɗa labarai ta kasa NBC Malam Balarabe Illela ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a Talata a Abuja.

Balarabe Illela ya ce matakin da shugaba Buhari ya ɗauka na sahalewa gidajen Talabijin da Rediyon ya yi daidai da dokokin hukumar ta NBC da aka yi wa kwaskwarima na shekarar 2004.

Ya kara da cewa yanzu haka dai kafofin yada labarai na Redio da Talabijin a ƙasar nan sun kai 625.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!