Connect with us

Labarai

An kama masu garkuwa da masu yi musu leƙen Asiri a Katsina

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kama wasu masu garkuwa da mutane su biyu da kuma masu kai musu rahoton sirri.

Kakakin rundunar SP Gambo Isah ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Talata ta cikin wata sanarwa daya fitar.

‘‘Lokacin da muka kama su mun kuma samu nasarar tseratar da mutum 10 da aka yi garkuwa da su tare da wasu shanu’’.SP Gambo Isah.

Yace cikin waɗanda suka kama akwai kwamandan masu garkuwa da mutane da suka jima suna nema Ibrahim Samaila da aka fi sani da Yalo wanda yayi hijira ya koma Daji da zama sai kuma Basiru Mu’azu.

Ya ƙara da cewa sun kama Yakubu Abubakar da Murtala Umar da suka ƙware wajen bai wa masu garkuwa rahoto da kuma wani ma’aikacin lafiya da yake yi musu magani idan sun sami rauni a Daji.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!