Labarai
Buhari ya amince da fitar da naira biliyan 10 don yin kidaya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da fitar da kudi naira biliyan goma don ci gaba da shirye-shiryen ayyukan kidaya a sauran kananan hukumomi 546 a kasar nan da suka rage ba a kai ga tantancewa ba.
Shugaba Buhari ya kuma amince da fitar da wasu karin kudi sama da biliyan hudu don ci gaba da shirye-shiryen yadda za a gudanar da kidayar al’ummar kasar nan, nan ba da dadewa ba.
Mai rikon mukamin shugabancin hukumar kidaya ta kasa Eyitayo Oyetunji ne ya bayyanawa manema labarai hakan a birnin tarayya Abuja, game da shirin da hukumar ke yi a baya-bayan nan.
You must be logged in to post a comment Login