Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya bai wa ‘yan bindiga wa’adin watanni biyu da su mika wuya

Published

on

Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa ‘yan bindiga da ke aikata ta’asa a jihohin arewa maso yammacin kasar nan wa’adin watanni biyu da su mika wuya.

Gwamnan na Zamfara ya bayyana hakan ne yayin wani jawabi da ya gabatarwa al’ummar jihar a yammacin jiya talata.

Ya ce shugaba Buhari ya ba da wannan umarni ne ya yin wata ziyarar kwanaki hudu da ya kai birnin tarayya ABUJA abaya-bayan nan don tattaunawa da masu ruwa da tsaki game da mawuyacin hali da jihar ta Zamfara ke ciki.

Umarnin shugaban kasar na zuwa ne kasa da mako guda bayan da ya haramtawa sojoji shawagi a sararin samaniyar jihar ta Zamfara.

Haka zalika shugaban kasar ya kuma haramta sana’ar hakar ma’adinai musamman hakar zinare a jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!