Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

 Ina makomar Cristiano bayan ficewar Juventus daga Champions league?

Published

on

Cristiano Ronaldo da kungiyarsa ta Juventus sun gaza kai bantensu a gasar zakarun turai (Champions League), duk kuwa da nasarar da kungiyar ta samu akan takwararta ta FC Porto da ci uku da biyu a wasan zagaye na kungiyoyi 16 da aka gudanar a filin wasa na Estadio Della Appi da ke birnin Turin a daren jiya talata.

Zura kwallaye har sau biyu a bugun tazara da dan wasa Sergio Oliveira ya yi, ya bai wa FC Porto damar tsallakawa zuwa zagayen daf da kusa da na karshe (quarter final).

A wasan farko da aka gudanar a kasar Portugal kungiyar FC Porto ta samu nasara da ci biyu da daya yayin da a daren jiya Juventus ta samu nasara da ci uku da biyu, sai dai duk da haka FC Porto ce ta tsallaka zagaye na gaba sakamakon samun samar zura kwallaye biyu a ragar Juventus a gidanta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!