Connect with us

Labarai

Buhari ya nemi gwamnoni su tilastawa al’umma amfani da face marsk

Published

on

Shugaban kasa muhammadu Buhari ya bukaci gwamnonin kasar nan dasu tilastawa al’umominsu yin amfani da takunkumin rufe hanci da baki, a wani mataki na cigaba da yaki da cutar corona a fadin kasar nan.

Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar rahotan kwamitin kar ta kwana dake yaki da cutar Covid 19 karkashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha jiya a Abuja..

Sai dai Shugaban kwamitin Boss Mustapha yayin mika rahotan kwamitin ga shugaban kasa yace ana samun cigaba a fadin kasar nan wajen yaki da cutar ta Covid 19.

Boss Mustapha ta cikin rahotan na kwamitin ya bayyana cewa  zasu bayyana mataki na gaba da cutar take a fadin kasar nan domin daukar mataki na gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!