Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnati zata biya ma’aikatan da suka yi aiki lokacin Corona alawus

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce zata fara biyan ma’aikatan da sukayi aiki don dakile cutar corona alawus-alawus dinsu na watan Yuni daga ranar 10 ga watan nan da muke ciki.

Ministan kwadago, nagarta da samar da ayyukan yi Dr. Chris Ngige ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da kungiyar likitoci ta kasa a birnin tarayya Abuja.

A cewar Ngige Gwamnatin zata fara biyan ma’aikatan ne daga ma’aikatan asibitoci guda Shida dake fadin kasar nan.

Chris Ngige ya ce ma’aikatar lafiya ta kasa da ofishin kula da kasafin kudin na gwamnatin tarayyada da ma’aikatar kudi na aiki domin shawo kan matsalar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!