Connect with us

Labarai

Buhari ya ce nan ba da dadewaba za’a komawa makarantu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce da zarar an dage dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi a kasar nan zata fara shirye-shirye kan yadda za’a koma makarantu a kasar nan.

Karamin ministan Ilimi Emeka Nwajiuba ne ya bayyana hakan a yayin da kwamitin shugaban kasa kan yaki da cutar Corona ke gudanar da taron manema labarai da ya saba a kullum, yana mai cewa, gwamnatin tarayya na bin matakan da suka dace ne, don bude makarantu a kasar nan gudun kar a yi gaggawa, hakan kuma ya jefa rayuwar al’ummar kasar nan cikin hadari.

Emeka ya kuma kara da cewa, har yanzu gwamnatin tarayya bata tsayar da tartibib lokacin da za’a koma makarantu ba, a don haka jama’a su yi watsi da duk waani rahoton komawa makaranta da ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani.

Idan dai za’a iya tunawa, tun a watan Maris din da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta rufe dukannin makarantun kasar nan, sakamakon yadda cutar Covid-19 ke kara karuwa a kasar nan.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,281 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!