Coronavirus
Mace-macen Kano ya faru ne sakamakon Cutar Covid-19 -Ministan Lafiya
Ministan lafiya Dr Osagie Ehanire ya ce kwamitin kar ta kwana da ma’aikatar lafiya ta kafa domin gano dalilan mace mace a nan Jihar Kano tsakanin watan Afrilu da Mayu ya kai mutum 979.
Osagie Ehanire ya ce kashi 50 zuwa 60 na mace macen ana ganin ya faru ne sakamakon cutar Covid 19.
Ministan na lafiya ya bayyana hakan ne a lokacin bayanai na yau da kullum da kwamitin kar ta kwana na shugaban kasa akan yaki da cutar Covid 19 ke gabatarwa.
Limamin Kano ya bukaci al’umma su rinka yiwa shugabanni addu’a
Covid-19: Dokar kulle ta taimaka wajen dakile cutar – Kwamishinan Lafiya
Dr Ehanire ya ce daukin da kwamitin yakai wasu jihohin arewacin Najeriya ya taimaka wajen rage kamuwar ma’aikatan lafiya.
Rahotanni sun yi nuni da cewa lokacin da aka bayar da rahotan mace macen gwamnayin jihar Kano ta karyata.
You must be logged in to post a comment Login