Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya gana da gwamnonin Arewa maso gabashin kasar nan

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na wata ganawa da gwamnonin Arewa maso gabashin kasar nan da manya hafsoshin tsoro a fadarsa dake birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa ganawar da shugaba buhari yake da masu ruwa da tsakin zata mayar da hankali ne akan matsalolin tsaro da suka addabi wasu sassan kasar nan.

Daga cikin wadanda shugaban kasar ya gana dasu sun hadar da mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari.

Sai gwamnan jihar Barno Farfesa Babagana Umara Zulum, da Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad da Gwamnan Gombe Inuwa Yahya da Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku. Sai kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni

Sauran sun hadar da Babban Hafson Tsaron kasar nan Janar Gabriel Olonisakin da baban hafson sojin kasar nan Laftanal Janar Yusuf Tukur Burtai da babban hafson sojin ruwa Admiral Ibok Ekwe Ibas, sai babban hafson sojin sama Air Marshal Sadique Abubakar da babban sefeto janar na ‘yan sandan kasar nan Mohammad Adamu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!