Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

NUPENG sun tsunduma yajin aiki a Legas

Published

on

Da safiyar yau ne direbobin tankar mai da iskar gas shiyyar jihar Legos NUPENG ta tsunduma yajin aikin sai Baba ta gani.

Shugaban kungiyar Mr Tayo Aboyeji ne ya sanar da hakan, yayin da yake zantawa da kamfanin dillanci labarai na kasa NAN.

Aboyeji ya ce, yajin ya biyo bayan saba alkawarin da gwamnatin jihar Legos ta kula da kungiyar, yana mai cewa a daren jiya Lahadi kungiyar ta yi zama na musamman da gwamnatin

Sai dai har aka kammala ba a kai ga cimma matsaya kan alkawuran nasu ba.

Ta cikin jawabin nasa, Aboyeji ya ce direbobin tankar mai ne kadai yajin aikin ya shafa, sakamakon yadda cinkoson hanyoyi ya hana manyan motocin yin aikin su yadda ya kamata.

Tun a ranar bakwai ga watan da muke ciki ne kungiyar ta bai wa ‘ya’yan ta umarnin tsunduma yajin aiki a yau Litinin ta cikin sanarwar hadin guiwa da shugaban kungiyar ta kasa Mr Williams Akporeha da kuma sakataren Janar Mr Olawale Afolabi suka fitar ga ‘ya’yan kungiyar sakamakon rashin cika musu alkawura da gwamnati yi.

Cikin alkawuran da suka sanya kungiyar tsunduma yajin aikin akwai yawan karbar na goro da jami’an tsaro ke yi ga direbobin kungiyar, da kuma cunkushe hanyoyin zirga zirgar manyan motocin.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!