Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya gana da shugabanin kasashen Afrika ta kafar Internet

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi sawun takwarorin shugabanin kasashen Afrika ta yamma kan tattaunawa wajen warware rikicin siyasa da ya dabaibaye kasar Mali ta kafar Internet.

A yau litinin ne dai shugabannin kasashen suka ci gaba da tattaunawa a babban birnin kasar ta Mali wato Bamako tare da bangarorin masu rikicin a teburin sulhu wanda aka fara tun a ranar Alhamis din makon da ya gabata.

Idan za a iya tunawa dai tun a ranar alhamis din da ta gaba ne aka cimma matsaya da niyyar za a ci gaba da tattaunawar a yau Litinin.

Tun a ranar Alhamis din kuma shugaban kasar Niger wanda shi ne shugaban kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afrika ta “ECOWAS” Mahamadou Issoufou ya bayyana cewa akwai bukatar kungiyoyin kasar su yi duk mai yiwuwa wajen kawo karshen rikice-rikien da ya adabi kasar.

Shugabannin kasashen yammacin Afrika da suka hadar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita da kuma shugaban kasar Senegal Machy Sall

Sauran su ne, Nana Akufo-Addo na kasar Ghana sai kuma shugaban kasar Cote d’Ivoire Alassane Ouattara wadanda suka ziyarci kasar ta Mali don tattauna batu rikicin siyasa da ya addabi kasar, yayin da wakilan kungiyoyin rikicin da kungiyoyin cikin gida suka bayyana matsayar su akan rikicin.

Tun da fari dai tsohon shugaban kasar nan Goodluck Jonathan wanda kuma shi ne jagoran kwamitin sulhu na a kasar ta Mali ya kai ziyara kasar makwannin biyun da suka gabata inda ya bukaci masu gudanar da zanga -zanga a kasar da su dakatar tare da yi alkawarin cimma matsaya.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!