Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kwamitin daukar ma’aikata na Kano zai magance yin kutse – Abubakar General

Published

on

Kwamitin daukan ma’aikata a kananan hukumomin jihar Kano wanda gwamnatin tarayya zata  yi da ya kai  dubu dari bakwai da saba’in da hudu a jihohin kasar nan 36, ya ce zai mangance yin kutse a shirin samar da aiki  yi da za’a yi nan bada jimawa ba.

Sakataren yada labarai na kwamitin daukar ma’aikata na jihar Kano Abubakar Muhammad general ne ya bayyana hakan a yau, jim kadan bayan kammala shirin “Barka da Hantsi” na nan tashar freedom radiyo, wanda ya maida hankali kan yadda tsarin daukan matasan aiki zai kasance a jihar Kano.

A cewar general, kwamitin a nan Kano mai dauke da mutum Ashirin ya tsara rarraba form din shaidar samun gurbin aikin ga matasa don magance samun masu yin kutse a irin wannan sha’ani.

Abubakar Muhammad ya kuma ce, za a fara shirin ne a ranar daya ga watan Okotoba, kuma zai dauki tsawon watanni uku ana yin sa tare da biyan ma’aikata dubu Ashirin a kowanne karshen wata.

General Abubakar ya ce, kwamitin ya hada da sarakunan gargajiya da malamai da sauran masu fada aji, a don haka akwai bukatar al’ummar jihar Kano musamman wadanda suke da aiki su bai wa marasa aikin yi damar samun shiga shirin don magance matsalolin matasa marasa aikin yi a kasar nan.

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!