Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya kaddamar da Tambarin bikin cikar Najeriya shekaru 60

Published

on

Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani tambari da za a rika amfani da shi wajen gudanar da bikin ranar yancin kai a kasar nan dai-dai lokacin da kasar ke cika shekaru sittin da samun ‘yancin kai.

Shugaba Buhari ya kaddamar da tambarin ne ya yin zaman majalisar zartarwa ta kasa yau a Abuja.

Yayin zaman na yau ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da ministan cikin gida Ra’uf Aregbesola da ministan yada labarai da raya al’adu Alhaji Lai Muhammad sai kuma ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola dea sauran ministoci.

Idan dai za a iya tunawa tun a farkon watan satumbar da muke ciki ne gwamnatin tarayya ta bukaci yan kasar nan da su fito da sabbin dabaru a yayin bikin cikar kasar nan shekara 60 da samun ‘yancin kai wanda a wannan shekara aka yi mata take da “together at 60”.

A ranar daya ga watan Oktoba me kawa ne kasar nan ke cika shekara sittin da samun ‘yancin kai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!