Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

BUHARI YA KALUBALANCI TSOFFIN SHUGABANNIN NAJERIYA

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya soki shugabannin kasar nan da suka gudanar da mulki tun bayan dawowa mulkin dimukuradiya a alif da dari tara da casa’in da tara zuwa shekarar dubu biyu da goma sha biyar, sakamakon caccakar gwamnatinsa da su ke yi a wannan lokaci.

 

Ta cikin jawabi da ya gudanar ga al’ummar Najeriya da misalign karfe bakiwa na safiyar yau, shugaba Buhari ya ce abin mamaki ne ace mutanen da suka dauki tsawon shekaru suna daidaita kasar nan, sune yau suke da bakin magana wajen sukar gwamnatinsa.

 

Muhammadu Buhari wanda ke jawabin a wani bangare na cikar kasar nan shekaru 60 da samun ‘yancin kai daga turawan burtaniya, y ace gwamnatinsa za ta ci gaba da mai da hankali wajen daukar matakai komai tsaurinsu kuwa don kai kasar nan tudun mun tsira.

 

Da ya koma ga batun tsame hannun gwamnati baki daya daga harkar man fetur wanda sanadiyar hakan farashin litar mai ya tashi, shugaba Buhari y ace, burinsa shine ganin kasar nan ta ci gaba da a don haka ba zai goyi bayan duk wani lamari da zai janyo gwamnati ta rasa kudade da za ta gudanar da ayyukan kasa ba.

 

Yana mai cewa babu dabara a ce Najeriya don kawai tana da arzikin man feur sannan shikenan sai ya kasance farashin mai yafi na kasar saudiya saukin farashi.

 

Shugaba Buhari ya kuma ce duk da halin da ake ciki a wannan lokaci amma farashin mai a najeriya yafi na kasashen Saudi Arebiya da Chadi da Nijar da kuma Ghana sauki sosai duk kuwa da cewa suma kasashe ne masu arzikin man fetur.

 

Shugaban na Najeriya ya kara da cewa, Najeriya fa ba mallakin shi bane ko mallakin wani mutum guda saboda haka akwai bukatar jama’ar kasa baki daya su hada kai wajen ciyar da kasars u gaba.

 

Ya ce gwamnatin sa tana ta aiki dare ba rana don ganin ta yaki fatara inda ta wani shiri na fitar da al’ummar kasar nan sama da miliyan dari daga kangin talauci cikin shekaru goma masu zuw.

 

Buhari ya kammala jawabin da yia ddu’a ga wadanda suka d\sadaukar da rayukansu wajen neman ‘yancin kasar nan da kuma ganin ta ci gaba da kasancewa a matsayin kasa guda.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!