Labarai
Mun kawo karshen matsalar tsaro dai-dai lokacin da Najeriya ke cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai – Ganduje
A yayin da ake bikin ranar samun yancin Kan kasar nan a yau Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce cikin nasarorin da jihar Kano ta samu a halin yanzu akwai tsaro sakamakon irin hadin kan da aka samu tsakanin jami’an tsaro da Kuma al’umma.
Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne yayin gudanar da bikin murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kan kasar nan da aka yi gudanarwa a filin Wasa na Kano pillars dake Sabon gari.
Gwamna Ganduje ya Kara da cewa jihar ta Kano zata ci gaba da kokari wajen inganta harkar lafiya, da harkokin sufuri da ilimi da Noma.
Ta cikin jawabin nasa ya kuma taya ‘yan Jihar Kano murnar cika shekara sittin da samun ‘yancin kan Najeriya.
Gwamna Ganduje ya bukaci al’umma da su cigaba da tabbatar da zaman lafiya musamman a tsakanin dukkan kabilun kasar nan don samun dorewar zaman lafiya.
Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa Gwamnan na cewa duk da an takaita taron saboda cutar Corona akwai bukatar al’umma su yi amfani da damar wajen gudanar da addu’o’in kariya daga cutar a kasar nan gaba daya.
You must be logged in to post a comment Login