Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan Manjo Janar Sama’ila

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyyar sa ga iyalan Manjo Janar Sama’ila Ilyasu bisa rasuwar sa.

Wannan na cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Femi Adesina.

Sanarwar na bayyana cewa marigayin soja ne da ya sadaukar da rayuwar sa wajen kare kima da mutuncin kasar nan da kuma tabbatar da zaman lafiya.

Shugaba Buhari ya kuma ce Marigayi Manjo Sama’ila mutum ne na gari, mai son ci gaban sakar nan da kuma iya shugabanci, kasancewar ya rike mukamin shugaban tawagar kwantar da tarzoma a kasashen Lebanon da jamhuriyar dimokradiyyar Congo.

Haka kuma Shugaban kasa ya kuma yi addu’ar ubangiji ya gafarta masa, ya kuma baiwa iyalan sa hakurin rashin sa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!