Connect with us

Labarai

Buhari ya yiwa jama’ar Kano ta’aziyyar marigayi Alhaji Shehu Rabi’u

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon taziyarsa ga iyalan shahararen dan kasuwarnan da ke nan Kano, Alhaji Shehu Rabi’u.

Wannan na cikin wata sanarwar mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musammam ga shugaban kasa kan kafafen yada labarai malam Graba Shehu.

A cewar sanarwar, shugaba Buhari ya ce mutuwar marigayi Alhaji Shehu Rabi’u babban ra shi ne ga al’ummar jihar Kano da ma kasa baki daya, a don haka ya bukaci al’umma da su yi wa marigayin addu’ar samun dacewa.

Sanarwar ta kuma ce, shugaba Buhari ya kuma mika sakon taziyarsa ga iyalan marigayi Isiyaka Rabi’u da kuma shugaban rukunin kamfanonin BUA Alhaji Abdulsamad Isiyaka Rabi’u.

Haka zakika sanarwar ta kuma mika sakon taziyarsa ga gwamnatin jihar Kano hadi da masarautar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!