Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya umarci a gaggauta kawo karshen matsalar tsaro a Zamfara

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci mashawarcinsa kan harkokin tsaron Manjo Janar Babagana Munguno da gaggauta tsara yadda za a kawo karshen haren-haren ‘yn bindiga a Jihar Zamfara.

Wannan na cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar jiya.

Sanarwar ta ce nan ba da jimawa ba za a gudanar da wani taro na musamman domin tattauna yadda ake gudanar aikin hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba a Jihar ta Zamfara.

Wadanda za su halarci taron sun hada da Janar Babagana Munguno mai ritaya da ministan tsaro Manjo Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya, sai ministan harkokin cikin gida Ra’uf Aregbesola da kuma ministan tama da karafa Olamilekan Adegbite.

Haka zalika akwai shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta kasa NIA da takawararta ta DSS.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!