Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya zargi ‘yan Najeriya da haifar da rikice-rikice a wasu jiohin

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zargi wasu ‘yan Najeriya da yin tasiri wajen haifar da rikice-rikicen da ake gani a sassan kasar nan.

 

A cewar shugaba Buhari nan ba dadewa ba za a shawo kan matsalar ta hanyar amfani da karfi da kuma tasirin bayanan sirri don a gano su, kuma a magance su.

 

Shugaban na bayyana hakan ne a yayin da yake ganawa da gwamnonin arewa masu yammacin kasar nan a jiya Talata, don tattauna batutuwan da suka shafi harkokin tsaro a jihohin nasu.

 

Ya ce, sha’anin tsaro abin damuwa ne matuka a don haka gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiki tukuru don dakile ayyukan masu tada kayar baya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!