Labarai
Buhari zai kashe Biliyan Dari da Hamsin ga Titunan manyan hanyoyi
Gwamnatin tarayya zata kashe Biliyan Dari da Hamsin wajen yin aikin tituna arba’in da hudu na manyan hanyoyi a fadin kasar nan.
Karamin ministan aiyyuka da gidaje Injiniya Abubakar Aliyu, ne ya bayyana haka a birnin tarayya Abuja, ya yin ganawar sa da manema labarai.
Aikin wanda za a gudanar da shi a fadin kasar nan, kudaden gudanar dashi zasu fito ne daga tsarin Inshora na Islama Sukuk, wato Sukuk Bond, da za a karba daga ofishin lura da basussuka na kasa.
Injiniya Aliyu, wanda ya tattauna da ‘yan jaridu a wajen taron tsare-tsare na kasa da cigaba, ya ce duba da yanayi na karancin kudade da ake fuskanta hakan ta sa gwamnatin tarayya ta samu hanyar gudanar da ayyukan da ta dauko, tare da samun hanyoyin kudaden gabatar dasu.
Ministan ya kara dacewa, daga shekarar dubu biyu da sha bakwai zuwa da sha takwas, gwamnati ta kashe Biliyan Dari biyu, shima bisa tsarin inshorar na Sukuk, a hanyoyin kasar nan guda Hamsin da takwas, wanda ashirin da biyar daga ciki anyi su a shekarar dubu biyu da sha bakwai, ya yin da ashirin da takwas aka yi su a cikin shekara dubu biyu da sha takwas.
Ministan yace, a kokarin da gwamnati take na ganin an cike gibi da samun dai daito, ma’aikatar sa zata cigaba da gudanar da ayyukan tituna da gyara su a makarantun gaba da sakandire, ta hanyoyi daban-daban a makarantu 44, a fadin kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login