Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya siyowa Najeriya sabbin na’urorin wutar lantarki daga Jamus

Published

on

Ministan Lantarki na ƙasa Injiniya Abubakar D. Aliyu ya kai ziyara ƙasar Jamus domin gani da ido a katafaren kamfanin makamashi na duniya wato Siemens.

Yayin ziyarar ministan na duba manyan tashoshin lantarki na tafi da gidanka da gwamnatin tarayya ta siya domin inganta wutar lantarki a faɗin kasar nan.

Ministan ya jaddada aniyar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na ganin an kawo ƙarshen matsalar wuta, ta hanyar inganta tsarin raba wutar lantarki da kuma sayo sabbin na’urorin tranfoma masu ɗaukar nauyin wuta mai yawa.

Ministan da tawagarsa sun ziyarci masa’antar Siemens a birnin Berlin da kuma Frankfurt inda yayi kira ga kamfanin na Siemens ya hanzarta samar da na’urorin wutar lantarki da gwamnatin tarayya ta siya.

Labarai masu alaƙ:

Da ɗumi-ɗumi: Gwamnatin tarayya ta shawo kan matsalar lantarki

Buhari ya amince da kwangiloli 16 domin bunƙasa wutar lantarki

Injiya Abubakar Aliyu ya kuma ce, gwamnatin tarayya zata ci gaba da duba duk wasu hanyoyi da dabaru na tabbatar da cewa wutar lantarki ta inganta.

Yayin ziyarar ministan na tare shugaban kamfanin lantarki na ƙasa Mista Kenny Anuwe da kuma shugaban shirin ofishin aiwatar da sabon tsarin inganta wutar lantarki na ƙasa Injiniya Mustapha Balarabe Shehu.

Ministan lantarkin yayi amfani da wanann ziyarar wajen ganawa da ministoci da manyan jami’an gwamnatin Jamus domin neman haɗin gwiwa da tallafi wajen ingantawa da sabunta tsarin samar da lantarki a Nijeriya.

Wanann ziyara dai ta biyo bayan matakin shugaba Buhari na sayen manyan tashoshin lantarkin tafi-da-gidanka da kuma manyan transfoma na zamani domin inganta wutar lantarki.

A nasa ɓangaren Kamfanin na Siemens ya yaba da wannan ziyara, inda kuma yayi alƙawarin ganin an kammala samar da kayyakin da Najeriya ta siya cikin ƙanƙanin lokaci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!