Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari zai rabawa manoma bashi- Sabo Nanono

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce, za ta ribanya kokarinta domin manoman Najeriya su kara samun dabarun samun amfanin gona mai yawa musamman manoman shinkafa.

Ministan aikin gona da raya karkara Alhaji Sabo Nanono, ne ya bayyana hakan a yau Litinin yayin kaddamar da rabon tallafin kayan aikin gona na bana da aka gudanar ga manoman shinkafa a gundumar Tofai dake karamar hukumar Gabasawa wanda shirin habbaka aikin gona na APPEALS ya gudanar.

Haka kuma ministan ya bukaci manoman da suka ci gajiyar kayan da su tabbata sun yi amfani da su ta hanyar da ta dace, domin ribanya amfanin gonar da suke samu.

Alhaji Sabo Nanono ya ce, nan ba da jimawa ba gwamnatin tarayya za ta baiwa manoma bashin motocin aikin gona watau Tantan akan farashi mai saukin biya cikin wasu shekaru.

A nasa jawabin shugaban shirin na APPEALS na jihar Kano Malam Hassan Ibrahim ya ce, fiye da manoman shinkafa 60 ne suka ci gajiyar tallafin taki da iri da man kone ciyawa da maganin kwari da kuma wasu injinan casar shinkafa da na bada tazara tsakanin kunya da sauran kayan aikin gona.

Malam Hassan Ibrahim ya kara da cewa, a karkashin shirin an hada manoman da malaman gona da za su rika kula da shukar da suka yi har zuwa lokacin da za ta isa girbi inda ake sa ran za su noma Tan 380.

Wakilinmu Auwal Hassan Fagge, ya ruwaito cewa, babban jami’in shirin na APPEALS yace, shirin ya horar da manoman kan yadda ake amfani da sababbin kayan aikin gona na zamani domin bunkasa aikin noma.

Haka kuma taron ya samu halartar manoma da masu rike da sarautu gargajiya da dama na karamar hukumar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!