Connect with us

Labarai

Buhari zai rabawa manoma masara a Najeriya

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da rabawa manoma Tan dubu Talatin na masara da aka debo daga rumbun ajiye kayayyakin abinci na kasa.

Hakan na cikin sanarwar da Shugaba Buhari ya wallafa a shafin sa na Twitter a yau Alhamis.

Shugaba Buhari ya ce hakan zai saukakawa manoma musamman masu kiwo wajen ciyar da dabbobin su cikin farashi mai sauki.

Cikin jawabin nasa ya bayyana cewa, yana sane da halin da ake ciki na tashin farashin abinci a kasar nan, ya kuma alakanta hakan da yadda annobar corona ta durkusar da tattalin arziki.

Buhari, ya kuma ce zai yi duk me yiwuwa don ganin an sauko da farashin kayayyakin abinci a kasar nan.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!