Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari zai sake ciyo bashin sama da Dala biliyan 4

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya buƙaci majalisar dattijai da ta amince masa ya ciyo bashin sama da Dala biliyan huɗu da yuro miliyan ɗari bakwai da goma.

Cikin wata takarda da shugaba Buhari ya aikewa majalisar dattijai na ɗauke da buƙatar ta sahale masa rancen kuɗaɗen.

Shugaban majalisar Sanata Ahmad Lawal ne ya karanta wasiƙar a zaman majalisar na yau Talata.

Wasiƙar ta bukaci majalisar ta amince da aro kuɗin kamar yadda ta amince aka ciyo bashin dala miliyan ɗari da ashirin da biyar a shekarar 2018 da 2020.

A cewar wasikar amincewar zai bada dama wajen ci gaba da ayyuka a ƙasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!